|
Shirin Rana
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Gwamnatin Pakistan ta fara samar da motocin safa-safa, da na daukar kaya domin su taimakawa iyalan da suka guje ma rikici a kwarin Swat komawa gidajensu. Mutane kimanin miliyan biyu ne suka yi gudun hijira a lokacin hare-haren da sojoji suka rika kaiwa a kan mayakan Taliban a baya bayan nan.
Gwamnatin kasar Sin ta ce 'yan sanda sun kashe wasu 'yan kabilar Wiga su biyu a birnin Urumci. Ana cewa wannan lamarin shi ne mafi tayar da hankali da ya faru cikin 'yan kwanakin nan.
A Najeriya, ana can ana shirin cigaba da shari'ar da ake yiwa Henry Okah, madugun kungiyar MEND- mai ikirarin fafutukar kwatar 'yancin yankin Niger Delta mai arzikin mai, a wani yunkuri na ganin cewar an sake shi.
Yayin da ake shirye-shiryen sauraren shariar da ake yiwa jagoran na MEND, Henry Okah, kungiyar tasa ta MEND ta yi ikirarin kai hari akan wani wurin sauke mai dake Lagos. Ba kasafai dai kungiyar ta MEND ke kai hari a wajen yankin Nijer Delta ba.
A fagen siyasar Najeriya ganawar da tsohon shugaban kasar, kuma dan takarar jam'iyyar adawan ANPP a zaben shugabancin kasar, Janar Mahammadu Buhari mai ritaya yayi da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, na cigaba da jawo cace-kuce.
Lauyoyin jamhuriyar Nijar na gudanar da yajin aiki na yini guda, domin kokawa da matakin da shugaba, Tandja Mamadou ya dauka, na rusa kotun tsarin mulkin kasar. Daya baya shugaba Tandjan ya nada sabuwar kotun ta tsarin mulki.
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||