|
Demokaradiyya A Najeriya
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Shirye Shirye na Musamman Kan Cikar Shekaru Goma Da Maido Da Mulkin Demokaradiyya A Najeriya Ba Tare Da Sirkin Mulkin Soji
Ba.
Tsarin democradiyya na nufin gwamnati ta mutane wadda jama'a ke yankewa kansu shawara kan wanda zai wakilce su ko kuma ya shugabance su. Wannan wani tsari ne da jama'a ke da 'yanci ta fuskar siyasa wanda ya dogara kan tsarin gudanar da gasa ta zabe kuma bisa gaskiya. A cikin shekaru 10 da suka shige Nigeria tana bin tsarin democradiyya, abunda ake ganin gagarumin ci gaba ne domin shine lokaci mafi tsaho da aka samu mulkin farar hula tun bayan da kasar ta karbi 'yancin kai daga Birtaniya a 1960. Daga ran 1 ga watan Mayun shekarar 2009 ne Sashen Hausa na BBC ya fara gabatar muku da rahotanni da hirarraki na musamman, kan shekaru goma da Nigeria ta yi tana bin tsarin democradiyya ba tare da surkin mulkin soja ba - abunda kuma zamu shafe wata guda muna yi. A wannan shafi za kuji jerin rahotanni inda muka duba nasarorin da aka samu da kuma kalubalen dake gaban Nigeria a yunkurin ta na tattabar ci gaba da kasancewa bisa wannan tafarki da masanan kimiyyar siyasa na duniya suka bayyana da cewa yana da matukar riba ga al'umma.
1 Ga Watan Mayu 2009 Tsarin na dimukradiyya dai tsari ne mai manufa ta bai daya a sassa dabam dabam a duniya. Sai dai wajen aiwatar da shi ne ake samun bambanci, musamman ma akan yadda 'yan siyasa da mahukunta ke ganinsa.
2 Ga Watan Mayu 2009 Tun lokacin da kasar ta sami 'yancin kai kusan shekaru arba'in da tara da suka wuce, a lokuta dabam-dabam an yi wa mulkin demokradiyyar karan tsaye, sakamakon juye-juyen mulkin da sojoji suka rika yi.Ga shirin Gane Mani Hanya na mussaman akan cikar shekaru goma da dorewar mulkin demokradiyya a Nijeriya .
3 Ga Watan Mayu 2009 Shirinmu na Taba Kidi Taba Karatu na wannan makon an gabatar dashi ne kacokan akan mulkin demokaradiyyar Najeriya.
4 Ga Watan Mayu 2009 Wani bangaren da ake ganin ya kamata ya ci gajiyar mulkin demokradiyyar shine: yankunan karkara, wadanda bisa tsarin mulki
ke karkashin kananan hukumomi.
5 Watan Mayu 2009 Tun lokacin da Najeriya ta sami 'yancin kai kusan shekaru arba'in da tara da suka wuce, a lokuta dabam-dabam an yi wa mulkin demokaradiyyar karan tsaye, sakamakon juye-juyen mulkin da sojoji suka rika yi. Shekaru goman da aka yi a jere ana mulkin farar hula a Najeriya shi ne mafi tsawo a tarihin kasar. Kokarin da aka yi a karo na farko da na biyu da na ukku basu yi karko kamar na wannan karon ba. Wannan ne ya baiwa 'yan kasar da dama kwarin gwiwar yin hasashen samun habakar demokaradiyya a kasar, duk kuwa da irin matsalolin da tsarin ke fuskanta.
6 Ga Watan Mayu 2009 Rawar da Shugabannin gwamnati ke takawa a tsarin mulki irin na demokaradiyya na da muhimmanci ga cigaban rayuwar 'yan kasa da tattalin arzikin kasar. To amma a Najeriya, duk da cewa kasar ta shafe shekaru goma kan turbar demokaradiyya, rashin kyakkyawan Shugabanci ne masana harkokin siyasa suka ce Ummul-haba'isin matsalolin da kasar ke fuskanta. Nijeriya dai kasa ce dake bin tsarin siyasa mai matakai uku na gwamnati, to amma, masana harkokin siyasa, sun bayyana cewa dukkan Shugabannin matakan gwamnatocin kasar, suna yin karan-tsaye ga tanade-tanaden tsarin na demokaradiyya, abinda shugabannin suke musantawa. To kowacce rawa ya kamata Shugabannin a matakan gwamnatocin ukku su taaka? Ina kuma masu tsawatawa musu da ake batun suna saba ma tsarin na demokaradiyya?
7 Ga Watan Mayu 2009 Tun daga lokacin da aka yi nasarar kawar da mulkin soja a Najeriya ne, wato shekaru goma da suka wuce, 'yan kasar suke cin moriyar mulkin farar hula. Duk da korafin da wasu ke yi na cewa 'yan siyasa sun kasa magance matsalolin kasar, akasarin 'yan Najeriyar na nuna cewa mulkin dimukradiyyar ne suke bukata.
8 Ga Watan Mayu 2009 Jam'iyyun siyasa sune shika-shikan kafa gwamnatin dimukradiyya. Akwai fiye da jam'iyyu hamsin a Najeriya, amma kalilan daga cikin sune keda kujerun mulki ko na wakilci a majalisun dokokin kasar. Wasu daga cikin jam'iyyun sun samo tushe ne daga tsaffin jam'iyyun siyasar kasar, amma yawancinsu, an kafa sune a cikin 'yan shekarun nan. Masana da dama na ganin cewa batun akida ya gushe a tsarin jam'iyyun kasar.
9 Ga Watan Mayu 2009 Gudanar da zabukan cikin gaskiya da adalci na daga cikin abubuwan da ke kawo inganci a tsari irin na mulkin demokaradiyya, saboda hakan zai baiwa masu zabe damar kafa irin gwamnatin da suke so da zata ja ragamar mulkin a inda suke. Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya nazari akan yadda yakamata zabuka su kasance a Najeriya
11 Ga Watan Mayu 2009 Wani babban abinda ke bambanta mulkin soji da na farar hula shi ne wanzuwar majalisun dokoki. A tsarin dimukradiyya dai hakkin majalisun dokokin ne su kafa sabbin dokoki; su gyara wadanda ba'a gamsu dasu ba; su kuma sa-ido ga abubuwa da jami'an gwamnati ke yi, don tabbatar da ganin cewa ba a ci amanar jama'a ba. To, ko majalisun dokokin Najeriyar na yin hakan a shekaru goma na wannan mulkin farar hular?
12 Ga Watan Mayu 2009 Yawan zarge-zargen cin hanci da rashawa na daga cikin matsalolin da suka addabi majalisar dattawan Najeriya a shekaru goma na wannan mulkin farar hular. A kan hakan nema wasu daga cikin shugabannin majalisar suka rasa mukamansu; wasu 'yan Najeriya kuma su ka yi zargin cewa mutuncin majalisar ya zube. 'Yan majalisar dattawan dai sun sha musunta hakan, wasunsu kuma na danganta rigingimun shugabancin majalisar ne akan tsoma bakin bangaren zartarwa.
13 Ga Watan Mayu 2009 Gudanar da bincike na daya daga cikin ayyukan da tsarin mulkin Najeriya ya tanadarwa 'yan majalisun dokokin kasar. Majalisar wakilai data dattawan kasar suna nuna cewa sun dukufa wajen wannan aiki. To saidai 'yan Najeriya da dama na korafin cewa har yanzu hakan bai haifar da komai ba. Wasu ma na zargin cewa neman cimma burin siyasane kesa ake kafa wasu kwamitocin binciken
14 Ga Watan Mayu 2009 Babban kalubale ga mulkin dimukradiyya a Najeriya shine batun gudanar da sahihin zabe a kasar. Kusan anyi amannar cewa tunda aka sake komawa mulkin farar hula shekaru goma da suka wuce, an kasa gudanar da sahihin zabe a kasar. Rashin gudanar da sahihan zabene ke haddasa yawancin rigingimun siyasar kasar, ya ke kuma bata mata suna a idon duniya. Gwamnati na batun gyara tsarin gudanar da zabe a kasar, amma wasu na ganin cewa gyaran bai kai yadda ake bukata ba.
15 Ga Watan Mayu 2009 Daya daga cikin sauye sauyenda ake son yiwa tsarin gudanar da zabe a Najeriya shine baiwa dan takara mai zaman kansa, wato indipendaa, damar tsayawa zabe. A dokokin zaben da ake amfani dasu yanzu dai, jam'iyyun siyasa ne kawai ke da ikon tsaida mutum takara, to amma yanzu gwamnatin kasar na neman sauya hakan domin baiwa 'yan takara masu zaman kansu 'yancin yin takarar mukamai tun daga na majalisar dokoki har ya zuwa kujerar shugaban kasa.
16 Ga Watan Mayu 2009 Wani batu dake jan hankalin ‘yan Najeriya a wannan lokacin na mulkin demokaradiyya shine batun yadda jam’iyyun siyasa ke gudanar da harkokinsu mussamman ta yadda ake tsayarda ‘yan takara da kuma batun tarukan da ake zaben shugabannin jam’iyya, inda a lokuta da dama ake zargin cewar masu riko da mukamman gwamnati kan yi amfani da kujerunsu wajen nada wadanda suke so, abinda suka sha musantawa.
18 Ga Watan Mayu 2009 A harkar gudanar da mulki a Najeriya, hakkin majalisun zartawar ne su aiwatar da tsare-tsaren gwamnati, majalisun dokoki kuma su sa ido ga abinda ke wakana. Manyan ayyukka na kasa sun dogara ne a kan majalisar zartawa ta tarayya, karkashin jagorancin shugaban kasa. Hakkin ministoci ne da sauran makarraban gwamnatin tarraya su gudanar da ayyukan da shugaban kasa ya basu, a kan yadda tsarin mulki ya shimfida. A shekaru goma da sake kafa mulkin farar hula ba yankewa a Najeriyar, jami'an gwamnatin tarayya sun dade suna ikirarin cewa ana aiwatar da tsarin bisa ka'ida, to amma 'yan kasar da dama na nuna tababa a kan hakan.
19 Ga Watan Mayu 2009 Tun komawar Najeriya ga mulkin Demokaradiyyane majalisun Dokokin kasar ke yunkuri daban-daban don gyaran-fuska ga kundin tsarin mulkin kasar amma babu wanda ya yi nasara. A baya-bayan nan ma majalisun dokokin kasar sun yi kamar za su yi, amma sai maganar ta lafa. Ko a ina matasalar take?
20 Ga Watan Mayu 2009 Abu ne da ya zama al`ada a duk lokacin da wata kasa ke gudanar da zabe, ayarin `yan sa-ido kan yi tururuwa zuwa kasar don duba yadda zaben ke gudana. A Najeriya ma ayarin masu sa-ido na kasa da kasa sun ziyarci kasar a manyan zabubbukan da ta gudanar a cikin shekaru goma da komawarta ga mulkin Demokuradiyya.
21 Ga Watan Mayu 2009 A cikin shekarun goman da suka shige, Najeriya na fuskantar kalubale daban-daban a yunkurin kasar na tabbatar da dorewar tsarin da masana kimiyyar siyasar duniya suka yi imanin shi ya fi dacewa ga ci gaban al'umma - wato tsarin democradiyya. Daya daga cikin manyan kalubalen demokaradiyya a Najeriya a wadannan shekaru kuwa, ita ce siyasar yanki ko salon karba karba wajen rabon mukamai, abunda wasu ke ganin yana tauye manufar demokaradiyya.
22 Ga Watan Mayu 2009 Cin Hanci da rashawa na daga cikin munanan abubuwan da tsari irin na demokaradiyya ke kokarin kawarwa. Ganin cewa yanzu haka an shafe shekaru goma kenan Najeriya na kan tsarin demokaradiyya, to ko yaya matsalar ke hana ruwa gudu?
23 Ga Watan Mayu 2009 Matsalar zargin cin hanci da rashawa ga shugabanni na daga cikin dinbim matsalolin da suka da baibaye harkokin siyasar Najeriya a cikin shekaru goma da kasar ta kwashe tana gudanar da mulkin demokaradiyya babu kakkautawa, kuma shirin Gane Mani Hanya na wannan makon yayi nazari ne akan wannan matsalar.
25 Ga Watan Mayu 2009 Batun sarrafa dukiyar kasa na daga cikin manyan abubuwan da ke kan gwamnatin tarayyar Najeriya. Tsarin mulki ya dora manyan
ayyukan kasa ne a kan gwamnatin tarayyar, domin itace ke da kaso mafi girma na dukiyar kasar.
26 Ga Watan Mayu 2009 Tun komowarta ga tafarkin demokaradiyya gwamnatin Najeriya ta fito da shirin samar da ilimi na bai daya, wato UBE ne da nufin wadata illahirin yaran kasar da ilimin firamare da kuma na karamar sakandare nan da sherara ta dubu biyu da goma sha biyar. Gwamnatin kasar dai na kashe dubban miliyoyin nairori a kan shirin don cimma wannan buri. Sai dai masana na cewa zaiyi wuya Najeriyar ta samu biyan bukata, sakamakon abin da suka bayyana da rashin kyakkyawan shiri.
27 Ga Watan Mayu 2009 A Najeriya cikin shekaru goman da kasar ta yi da komawa ga mulkin demokuradiyya, gwamnatin kasar ta kai turakun wutar lantarki a birane da yankunan karkara masu yawa. Sai dai kuma al`ummar kasar na kukan cewa ba su taba fuskantar matsalar karancin wutar lantarki irin na wannnan lokaci ba. Gwamnatin Najeriyar ta sha yin alwashin magance matsalar tare da kashe makudan kudade, amma har yanzu al`umomin kasar da dama na cikin duhu.
28 Ga Watan Mayu 2009 Batun gudanar da sahihin zabe a Najeriya shine kalubale mafi girma a shekaru goman da aka shafe bayan maido da mulkin dimukradiyya a kasar. Akasarin 'yan Najeriyar sun yi amannar cewar ba a gudanar da sahihan zabuka a kasar yanzu. Sai dai duk da haka akwai wasu zabukan da aka yi a kasar inda 'yan kasar suka daage suka kaare kuri'unsu. Wannan ne ma ya kawo batun taken da ake kira: "a kasa, a tsare, a raka", wanda wasu ke nuni da cewa anyi a Jihar Bauchi. Ko hakan zai taimaka wajen kawo gyara a tsarin zabe a Najeriya?
29 Ga Watan Mayu 2009 A Najeriya yau ake bikin ranar demokaradiyya, wato ranar da shekaru goma da suka wuce kasar ta koma bisa tafarkin siyasar demokaradiyya. A kokarin kitse jerin rahotanni da shirye shirye na musamman da Sashen Hausa na BBC ke gabatar muku duk tsawon watan nan na Mayu, a halin yanzu zaku saurari tattaunawa ta musamman akan ita kanta siyasar demokaradiyya da irin fadi tashin da aka yi ta fama da shi a cikin shekaru goman da suka wuce.
30 Ga Watan Mayu 2009 Yanzu dai shekaru goma kenan da komawar Najeriya ga mulkin demokaradiyya ba kakkautawa amma dai jama`ar kasar na kukan cewa ba su ga wani sauyi a rayuwarsu ba. Masana dai na danganta wannan matsala da gazawar shugabanni wajen kyautata rayuwar al`umar kasar. Daga shekarar 1999 zuwa yanzu dai Najeriyar ta gudanar da manyan zabubbuka a kasar har sau uku, amma dukkansu masu sa-ido a kan harkokin zabe sun yi zargin cewa suna cike da magudi, al`amarin da masana ke cewa na matukar barazana ga dorewar dimukuradiyya a kasar. Shirin Gane Mani Hanya ya maida hankali ne akan makomar demokaradiyya a Najeriya.
Za ku iya tuntubarmu da ra’ayoyi ko shawarwarinku ta hanyar adireshinmu na e-mail wato hausa@bbc.co.uk |
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||