|
BBC Hausa A Karkara
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
Jihar Taraba dake yankin arewa maso gabashin Najeriya ta kasance jihar ta karshe a rangadin BBC Hausa a karkara, inda tawagar
ta ziyarci jihohi goma sha na yankin arewacin kasar.
A lokacin rangadinnamu, 'yan tawagar sun tattaro bayanai daga yankunan karkara guda arba'in da biyar, inda alummomin kauyukan suka bayyana abubuwan dake ci musu tuwo a kwarya da nufin jawo hankalin shugabannin ko zasu kawo musu dauki. Mun kirkiro rangadin BBC Hausa a karkara da nufin nunawa jama'ar karkara cewa suna da mahimmanci a aikace-aikacenmu, kuma mu sada zumunci tsakaninmu da masu sauraronmu. A karshe dai mun cimma dukkannin manufofinmu, inda kuma jama'ar yankunan karkaran da muka gana dasu suka maida shirin mallakinsu kuma suna masu bude zukatansu da kofofinsu a garemu. Ga Jamila Tangaza da karin bayani kamar yadda ta gabatar da shirin safe kai tsaye a kofar fadar Mai Martaba Sarkin Mumuye, Chief Ado Adamu Masang na biyu.
A rana ta ashirin na rangadin BBC Hausa a karkara tawagar ta yaa da zango ne a kauyen Dogon Ruwa na cikin karamar hukumar Kaltungo ta jihar Gombe. Al'ummar kauyen na fama ta matsi na yau da kullum sakamakon karancin ababen more rayuwa, kuma ta hanyar ayyukan gayya suka gina dakin shan magani a kauyen , sai dai babu magungunan a cikin sa. Bugu da kari basu da hanyar mota da makaranta faramare. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
A ranar asabar ashirin da takwas ga watan maris, tawagar BBC Hausa a karkara ta yaa da zango ne a jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya. Tawagar ta ziyarci kauyen Shole Gwai-Gwai na cikin karamar hukumar Nafada, inda aka gabatar da shirin rana kai tsaye kuma mutanen kauyen suka koka akan rashin ababen more rayuwa kamar wutan lantarki da ruwan fanfo da dakin shan magani da makarantar faramare, inda suka mika kokon bararsu ga gwamnati don ta dube su da idon rahama. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
Tawagar BBC Hausa a karkara a ranar alhamis , ashirin da shida ga watan maris ta yaa da zango ne a kauyen kurna na karamar hukumar Busari ta jihar Yobe. Shugaban tawagar Jamila Tangaza ta gabatar da shirin rana kai tsaye daga cikin kauyen na kurnawa, inda mutanen kauyen suka koka game da rashin kulawar gwamnati wajen magance musu matsalolin dake addabansu, kamar batun kwararowar hamada, da karancin ruwan sha da makarantu da kuma asibiti. Aliyu Abdullahi Tanko ya gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
A ranar laraba, ashirin da biyar ga watan maris wato rana ta goma sha bakwai na rangadin BBC a karkara, tawagar ta yaa da zango ne a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya. Kiddiga da aka fitar sun nuna cewar jihar Yobe na daga cikin jihohin kasar da suka fi fama da talauci, sannan kuma batun gurguzowar hamada , da karancin ruwa da sauraran ababen more rayuwa na daga cikin matsalolin da al'ummar jihar ke fuskanta. Tawagar BBC a karkara ta ziyarci kauyen Tulu Tulu dake karamar hukumar Yusufari, kauyen da jamaarta a yawancin lokuta ke tsallakawa jamhoriyar Nijar don neman magani da kuma zuwa makarantar boko. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
A karon farko tunda aka fara rangadin BBC Hausa a karkara, shugaban tawagar Jamila Tangaza ta gabatar da shiri har biyu daga cikin kauye guda daya. An dai gabatar da shirin dare na ranar litinin ashirin da uku ga watan maris da kuma shirin safe na ranar talata ashirin da hudu ga watan maris duk a kauyen Sakarma dake kamar hukumar Kiru ta jihar Kano. Mutanen kauyen sun gabatar da matsalolinsu mussaman rashin isashen takin zamani abinda ke kawo musu cikas ga harkar noma da suka dogara da ita wajen tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
A ranar litinin ashirin da uku ga watan maris, tawagar BBC Hausa a karkara ta yaa da zango a jihar Kano wacce itace jiha ta karshe na yankin arewa maso yammacin Najeriya a jerin jihohin da rangadin BBC ya shirya. Alkaluman kidaya da gwamnatin kasar ta fitar a shekara ta dubu biyu da shida sun nuna cewar jihar Kano ta fi kowacce a Najeriya yawan jama'a a cikin kasar. Sai dai yawancin masana'antun jihar da suka bunkasa ada, sun daina aiki tun shekaru goma sha biyar da suka wuce, galibi saboda rashin wadatacciyar wutar lantarki abinda ke barazana ga cigaban jihar a yanzu. 'Yan tawagar rangadin na BBC a karkashin jagorancin Jamila Tangaza sun ziyarci kauyen Bodar Ali dake karamar hukumar Kura inda aka gabatar da shirin rana kai tsaye. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
Rangadin BBC Hausa a karkara zuwa kauyukan yankin arewacin Najeriya, a rana ta goma sha hudu wato ashirin da biyu ga watan maris, ta yaa da zango ne a kauyen Pampa'ida a karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna. Sai dai sabanin duka kauyukan da tawagar ta ziyarta, kauyen Pampa'ida nada ababen more rayuwa sakamakon hadin gwiwan hukumar bunkasa cigaba ta majalisar dinkin duniya wato UNDP da kuma gwamnatin jihar Kaduna da su kansu al'ummar yankin. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
A ranar asabar ashirin da daya ga watan maris tawagar ta yaa da zango ne a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya. Kaduna garin gwamna kamar yadda ake yiwa jihar lakabi, itace shalkwatan arewacin kasar, kuma a cikin ta ne Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello a matsayinsa na Pirimiyan jihar arewa ya mulki shiyyar. Tawagar ta ziyarci kauyen Rubuci a karamar hukumar ta Zariya, inda kuma aka gabatar shirin rana kai tsaye daga kauyen. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
A rana ta goma sha biyu na rangadin BBC hausa a karkara, tawagar ta ziyarci kauyen Siyori na karamar hukumar Garki a cikin jihar Jigawa. Kafin 'yan tawagar su isa kauyen saida suka amsa gayyatar mai martaba Sarkin Ringim,Alhaji Sayyadi Muhammadu Ringim, wanda ya gayyacesu domin ya nuna goyon bayan sa ga shirin na BBC hausa a karkara. Tawagar bayan ta bar fadar mai martaban, sai ta garzaya cikin kauyen na Siyori inda aka gabatar da shirin rana kai tsaye. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka gudana a kauyen.
Tawagar BBC Hausa a karkara ta ziyarci jihar Jigawa dake arewa maso yammacin kasar a ranar alhamis goma sha tara ga watan maris, jihar da kiddiga ta nuna cewar tana daga cikin jihohi goma da suka fi fama da talauci a Najeriya. Tawagar ta yaa da zango ne a kauyen Fadi Bara dake karamar hukumar Babura, kauyen da babu wutan lantarki da dakin shan magani. An gabatar da shirin rana kai tsaye a kauyen, amma ga Habiba Adamu dauke da wasu daga cikin abubuwan da suka wakana.
A rana ta goma na rangadin BBC Hausa a karkara, tawagar ta yaa da zango ne a kauyen Daba dake karamar hukumar Maidawa ta jihar Katsina. Jamila Tangaza wacce ta jagorancin sauran 'yan tawagar , ta tattauna ne da wakilan al'ummar kauyen da shugabanninsu a shirin rana kai tsaye,inda kuma suka bayyana matsalolin dake addabansu. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen.
Rangadin BBC Hausa a karkara a ranar talata goma sha bakwai da watan maris ta shiga cikin jihar Katsina dake arewacin kasar, kuma wacce ke makwabtaka da jamhuriyar Nijer. Tawagar daga isanta jihar ta yaa da zango ne a kauyen Indukum dake karamar hukumar Mani, inda kuma tare da wasu jama'ar kauyen suka dunguma zuwa kasuwar mashi wacce ke ci a ranar. Shugaban tawagar Jamila Tangaza ta gabatar da shirin rana kai tsaye a kasuwar mashin, inda jama'a soka bayyana damuwarsu akan abubuwan dake ci musu tuwo a kwarya. Habiba Adamu ta gutsuro mana wasu daga cikin abubuwan da suka wakana a kasuwar ta mashi da kuma zaman yau da kullum na mutanen kauyen.
A rana ta takwas wato goma sha shida ga watan maris, tawagar ta ziyarci kauyen Kurungunki dake karamar hukumar Talata Mafara na jihar Zamfara. 'Yan tawagar sun gana da mutanen kauyen kuma sun gani da idanunsu yadda al'ummar kauyen ke tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum, inda suke fama da matsalar rashin wutan lantarki, da dakin shan magani da ruwan sha da kuma rashin hanyar mota. A karshen tattaunawar, mutanen kauyen dai sun gabatar da bukantunsu ga shugabanni akan ababen more rayuwa mussaman a gina musu asibiti da makarantar karantun 'ya'yansu. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a rangadin.
A yayinda rangadin BBC Hausa a karkara ya shiga rana ta bakwai , tawagar ta yaa da zango ne a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya. Tawagar ta ziyarci kauyen Gabai na cikin karamar hukumar Birnin Magaji ,inda suka tattauna da al'ummar yankin akan matsalolinsu na karancin ababen more rayuwa da kuma fatarsu ga shugabanninsu. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a rangadin.
A rana ta shida wato asabar goma sha hudu ga watan maris, tawagar BBC Hausa a karkara ta ziyarci kauyen Burkussuma dake karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato. Koda yake babu wutan lantarki a kauyen, amma dai suna da makarantar faramare guda daya da aka kafa tun zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya, Alhaji Shehu Shagari, sai dai har yanzu ba a gina aji ko guda daya ba. Sai dai sabo da rashin kyawon yanayi da kuma fama da iska ba a su samu damar kafa wayar tauraron dan Adam ba, abunda ya hana mu gabatar da shirin rana kai tsaye kamar yadda muka saba. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a rangadin.
Tawagar BBC Hausa a karkara, a ranar juma'a goma sha uku ga watan maris, ta yaa da zango ne a jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya, kuma jihar itace cibiyar daular Usmaniyya. Tawagar kuma ta ziyarci kauyen Miyal Yako dake karamar hukumar Goronyo a cikin jihar, inda aka gabatar da shirin rana kai tsaye, kamar yadda akayi a sauran kauyuka. Al'ummar kauyen Miyal Yako na amfani ne da rakuma, da amalanken shanu da kekuna wajen zurga zurgan yau da kullum. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a rangadin.
A rana ta hudu wato alhamis goma sha biyu ga watan maris, tawagar ta ziyarci kauyen Botoro-Gadi na yankin karamar hukumar Maiyama a jihar Kebbi. Inda sai da suka ketara wani kogi da kafa, kafin su shiga kauyen. An gabatar da shirin rana kai tsaye a kauyen Botori Gadin kamar sauran kauyukan da tawagar ta ziyarta, inda al'ummar yankin suka bayyana kokensu ga shugabanni akan abubuwan dake ci musu tuwo a kwarya, kamar matsalar rashin gada, da asibitoci da makarantu da tsabtataccen ruwan sha. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a rangadin.
Tawagar BBC Hausa a karkara, a ranar laraba ta yaa da zango ne a jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya, jihar da ke makwabtaka da jamhuriyar Nijar da jamhuriyar Benin. Tawagar ta ziyarci kauyen Tudun Bude dake karamar Koko Besse , inda aka gabatar da shirin rana kai tsaye daga kauyen. Al'ummar kauyen dai na fuskantar matsaloli na rayuwa kamar yawancin kauyukan kasar,kuma suna amfani ne da amalanken shanu da kekuna da babura wajen zurga zurgan yau da kullum. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin abubuwan da suka wakana a kauyen na Tudun Bude.
A rana ta biyu wato talata goma maris, tawagar ta ziyarci kauyen Leshigbe dake kusada madatsar ruwa ta Kainji dake karamar hukumar Borgu a jihar Neja. Inda aka gabatar da shirin rana kai tsaye a karkashin bishiya a kauyen. Kauyen na Leshigbe dai na fama da matsalar karancin ababen more rayuwa mussaman tsabtataccen ruwan sha da asibiti da hanyar mota, abubuwan dake kara kunci ga rayuwar mazauna kauyen. Habiba Adamu ta gutsuro mana kadan daga cikin muhimman abubuwan da suka wakana a rangadin.
Kamar yadda mukayi alkawari, a yau litinin tara ga watan maris muka shiga rangadin yankunan karkara inda zamu je jihohi 11 a cikin kwanaki 21. Tawagar tamu ta yaa da zango ne a jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Najeriya. Mun ziyarci kauyen Erena a karamar hukumar Shiroro, kauyen da babu wutar lantarki da sauran ababen more rayuwa, kuma jama'ar na samun ruwan-sha ne daga wata madatsar ruwa kwaya daya . Bugu da kari, babu hanyar mota da ta hada kauyen da wasu kauyuka sai dai a shiga ta kwalekwale. Sai dai suna da makarantar faramare mai ajujuwa biyu da kuma masallaci da aka ginasu ta hanyar ayyukan hadin kan al'umma.
Daga ranar 9 ga watan Maris mai zuwa, Sashen Hausa na BBC zai fara wani rangadi a jihohi goma sha daya na arewacin Najeriya. Rangadin dai zai mayar da hankali ne kacokam kan yankunan karkara. Daga cikin manufar wannan ziyara tamu kuwa har da:
• Sake jaddada mahimmancin da sashen Hausa na BBC ya dauki masu sauraronmu dake yankunan karkara. • Bada dama ga masu sauraronmu a yankunan karkarar da za mu ziyarta - domin su bayyana ra’ayoyinsu akan al’amuran dake damun su da nufin mika koke-kokensu ga mahukunta domin su share musu hawayensu tare kuma da basu dama wajen bayyana ra'ayoyin su akan abubuwan dake gudana a duniya. • Bada dama ga masu sauraronmu a yankunan karkara domin su ga yadda muke gabatar da shirye shiryenmu kai tsaye. • Kara kusantar da shirye-shiryenmu ga masu sauraronmu. A lokacin rangadin dai za mu rika watso muku shirye-shiryenmu kai tsaye daga kauyukan da za mu ziyarta, tare kuma da muhawara a kan irin halin da wasu mazauna wadannan karkarun suke ciki. Batutuwan da za mu tabo a irin wadannan muhawarorin kuwa sun hada da:
• Koma baya a sashen ilmi: Rashin makarantu, rashin kayan aiki, rashin kwararrun mallamai, rashin sanya ‘ya ‘ya mata a makarantu, da sauransu • Tabarbarewar harkokin kiwon lafiya: Rashin kwararrun likitoci ko ma rashin likitocin kwatata kwata, karancin magunguna, nisan asibitoci daga wasu kauyuka, dogaro a kan magungunan gargajiya, rashin kayan aikin likitanci na zamani, yawaitar mace-macen yara kanana da mata masu ciki da sauransu. • Lalacewar hanyoyi da motocin sufuri a yankunan karkara: Shan bakar wahala wajen safarar amfanin gona zuwa birane. • Karancin ruwan sha da na amfanin yau da kullum. • Noman rani da na damuna: Rashin samun isasshen taki da kuma tsadarsa. • Hanyoyin sadarwa na zamani • Sabbin dabarun kasuwanci na zamani. • Cutar Polio ko shan inna/Cutar Kanjamau/Cutar malaria • Dabarun kiwo na zamani. • Gurgusowar Hamada da sare itatuwa domin girki • Fari • Karancin wutar lantarki/Rashin wutar lantarkin kwata-kwata • Wakilci irin na siyasa • Bangar Siyasa • Cin moriyar Demokauradiyya • Da sauran batutuwa da ku masu sauraronmu za ku so a yi muhawara a kansu.
Matashiya: Za dai mu rika rubuta muku bayanai a kan yadda rangadin yake gudana a wannan shafin tare kuma da saka muku irin shirye shiryen da za mu rika watsawa a duk tsawon lokacin rangadin. Za ku iya tuntubarmu da ra’ayoyi ko shawarwarinku ta hanyar adireshinmu na e-mail wato hausa@bbc.co.uk. Sai ku kasance da mu. |
WASU SHAFUNAMMU
Ra'ayoyin Masu Sauraro20 Afrilu, 2007 | News
Rahoto Cikin Hoto20 Afrilu, 2007 | News
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||