|
Shirin Safe/Shirin Hantsi
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Shugaba Tanja Mammadu ya kaddamarda gaggamin zaben raba gardama mai cike da cecekuce a daran jiya, wanda sakamakon haka ne ya gabatar da jawabi ga 'yan kasar. An dai gudanar da kasaitaccen buki bude wannan gangamin na zaben raba gardamar a daren jiyan a birnin Yamai babban birnin kasar. A waje daya kuma, Lauyoyi a jamhuriyar ta Niger sun ce za su fara yajin aiki a yau Litinin, domin adawa da shirin shugaban kasar Mamadu Tanja na shirya zaben raba gardama, domin sauya kundin tsarin mulkin kasar. Lauyoyin sun ce, yajin aikin na su, nuna goyon baya ne ga kotun tsarin mulkin Niger wadda ta haramta gudanar da zaben raba gardamar. A Kamaru ma, wani bangare daga cikin al'ummar Niger mazauna Yaounde babban birnin kasar sun shirya wani gangami na nuna goyon baya ga shugaban kasar Nijar Tandja Mamadou wanda ke yunkurin zarcewa a kan karagar mulki bayan karewar wa'adinsa. Gangamin ya gudana ne a jiya a karamin ofishin jakadancin Nijar da ke Kamaru.
A Najeriya yayin da uwar jam'iyyar ANPP ke jiran sakamakon binciken wani kwamiti kan matsalolin da suka dabaibaye jam'iyyar, a jihar Bauchi ana cigaba da nuna wa juna yatsa kan rashin tagomashin ANPP, wadda a da ta yi farin-jini da kafa gwamnati a jihar. Tuni dai gwamnan jihar Mallam Isa Yuguda da wasu 'yan majalissa goma sha bakwai suka kauracewa jam'iyyar ta ANPP, a cigaba da yi mata kawatsatsai zuwa PDP mai mulki. Kura dai na cigaba da dabaibaye batun tsige mataimakin gwamnan jihar Bauchin Alhaji Garba Mohd Gadi, sama da mako daya bayan babban jojin jihar, Justice Sabo Sulaiman Darazo ya kafa kwamitin bincike na mutane bakwai domin wannan aiki.
A jahar Kebbi dake arewacin Najeriya kuwa, ana cigaba da kai ruwa rana tsakanin magoya bayan tsohon gwannan jahar Senator Muhammad Adamu Aliero da na gwamna mai ci yanzu Usman Dakingari. An dai jima ana zargin cewa akwai rashin jituwa tsakanin mutanen biyu. A Kwanan baya ne magoya bayan tsohon gwannan jahar suka kafa wata kungiya ta yada kudurorin shugaban kasa guda bakwai wato Seven Point Agenda, kungiyar da gwamnatin jihar ta soke.
Pira ministan kasar Japan Taro Aso ya yanke shawarar rushe majalisar dokokin birnin Tokyo, sannan ya kira babban zabe, bayanda jamiyyarsa ta sha kaye a zabukan majalisar birnin na Tokyo. A ranar Lahadin da ta gabata ne, jamiyyarsa ta Liberal Democrat (LDP) wadda ta mulki kasar Japan na tsawon karni guda da ya gabata, ta fadi a zaben majalisar dokokin birnin Tokyo. Sai dai kuma a nata bangare jamiyyar adawa ta Japan Democratic Party ta sami nakasu kan batun gutsiri tsomar kudi, inda jagoranta Yukio Hatoyama ya nemi gafarar jama'a bayan da aka gano sunayen wasu mutane da suka mutu a matsayin masu tallafawa jam'iyyar da kudade.
Kafafen yada labaru na kasar Korea ta Kudu sun bada rahotannin cewa, shugaban kasar korea ta Arewa Kim Jong-Il na fama da cutar sankarar tumburkuma cancer. Sai dai ba a tabbatar da sahihancin majiyoyin ba da suka fito daga kasashen China da Korea ta Kudu.
Wata kididdiga da BBC ta gudanar, ta nuna cewa goyon bayan 'yan kasar Birtaniya ga yakin da take yi da Taliban ya karu. Kididdigar ta zo ne a daidai lokacin da sojojin Birtaniyan ke mummunan batakashi a kasar Afghanistan da mayakan Taliban, al'amarin da ya kai ga karuwar sojojin Birtaniya da suka rasa rayukansu ko suka jigata.
An sake dage shirin harba kumbon Amurka zuwa sararin samaniya mai suna Endeavour, sakamakon rashin kyawun yanayi. Wannan shi ne karo na hudu da hukumar kula da harkokin sararin samaniyan Amurka NASA ta jinkirta harba kumbon daga cibiyar Kennedy Space Centre a Florida. Darektan dake kula da harba kumbon Pete Nickolenko shine ya bada sanarwa dakatar da shirin mintuna goma kafin a harba shi. |
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||