|
Shirin Yamma
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mutane biyar ne suka mutu a harin da 'yan bindiga suka kai a wani wurin sauke mai dake Lagos a Nijeriya. Wannan shi ne karo na farko da aka kai hari makamancin wannan a wajen yankin na Niger Delta dake samar da arzikin man Najeriya.
A Nijeriya, an saki jagoran 'yan bindigar yankin Niger Delta, Henry Okah daga gidan kaso, bayan da gwamnati ta yi watsi da tuhumar da take yi masa ta cin amanar kasa. Bayan da ya fito daga kurkuku ya musanta cewa shi ke jagorancin kungiyar, ya kuma bayyana cewar ba shi da koshin lafiya.
Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya fadi zuwa kasa da dala sittin a yau Litinin. Tun daga karshen watan jiya farashin ya fadi da kamar kashi sha tara cikin dari.
Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da wani kwamitin da zai kula da aikin kafa sabuwar gwamnatin jihar. Tuni dai majalisar dokin jihar ta Sokoto ta yi dokar kafa wannan jami'a.
A Jumhuriyar Niger, jama'ar kasar na cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da zaben rabagardama kan wani sabon kundin tsarin mulki, wanda ke janyo takaddama.
Rikicin siyasar da ake fama da shi a Niger ba yana jan hankalin 'yan kasar ne kawai ba, a'a, har ma da 'yan kasashen waje, musamman makwabtan Nijer din. Gwamnan jihar Jigawa a Najeriya, Alhaji Sule Lamido ya tofa albarkacin bakinsa kan halin da ake ciki a fagen siyasar Niger.
Akwai mu kuma da filin labarin wasanni.
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||