BBC navigation

Za a sanya Boko Haram cikin 'yan ta'adda

An sabunta: 22 ga Mayu, 2014 - An wallafa a 16:32 GMT
Wakilan Amurka da Burtaniya a kwamitin

'Yan Najeriya za su zuba ido suka tasirin ayyana Boko Haram a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, idan hakan ta faru

Majalisar Dinkin Duniya za ta yanke shawara kan bukatar da gwamnatin Nigeria ta gabatar mata, ta ayyana kungiyar Boko Haram a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Kasar ta gabatar da bukatar yin hakan ne a gaban Kwamitin sulhu na Majalisar, wanda zai yanke shawarar a ranar Alhamis.

Idan har Majalisar ta amince da bukatar, to kasashe mambobinta za su samu damar taka-birki ga harkokin kungiyar Boko Haram, musamman abin da ya shafi asusun ajiyar kudi da makamai.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya riga ya nemi kasashen duniya, su sanya duk takunkumin da suka dake kan kungiyar da shugabanninta, domin murkushe kungiyar.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.