BBC navigation

Afghanistan :'rikicin kasar zai munana'

An sabunta: 12 ga Mayu, 2014 - An wallafa a 03:28 GMT

Nan gaba a wannan shekaran ce za a rufe babban sansanin sojin Birtania da ke Helmand a Afghanistan

Wata kungiyar kwararrun masana ta yi gargadin cewa rikicin Afghanistan da ake yi da Taliban zai munana in har kasashen duniya ba su samar da kudaden samar wa kasar sojoji masu yawa ba.

Kungiyar ta International Crisis Group, ta ce, ko da ike ba lalle ba ne 'yan Taliban su sake kama manyan biranen kasar, to amma lamarin a yankunan karkara na da wuya.

A cewar kungiyar idan ba a bai wa dakarun Afghanistan din ba karin kayan aiki, mayakan Taliban za su iya sake kama yankuna da dama na karkara da zarar sojojin kasashen duniya sun fice daga kasar.

An fitar da rahoton kungiyar ne wanda ke dauke da gargadin a ranar da 'yan Taliban su ka sanar cewa za su kaddamar da sabbin hare-hare.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.