BBC navigation

Chibok: Mata za su yi gangami a Nigeria

An sabunta: 30 ga Aprilu, 2014 - An wallafa a 13:29 GMT
Matan da za su yi gangami a Abuja.

Gangamin wanda kungiyar Women For Justice and Peace za ta jagoranta zai bukaci gwamnati ta kara kaimi

A ranar Laraba wata kungiyar mata za ta jagoranci gangami na mata miliyan daya a Abuja, domin matsin lamba ga gwamnatin Nigeria game da ceton 'yan matan Chibok.

Za a fara gangamin ne da misalin karfe uku na yamma agogon kasar, inda matan za su yi jerin-gwano zuwa majalisar dokoki.

Haka kuma za su je ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro, domin mika wasiku zuwa ga shugaban kasa.

Haka zalika za a yi irin wannan gangamin a wasu jihohin arewacin kasar, ciki har da Kano wadda ta fi kowace jiha yawan al'umma a kasar.

Kwanaki 16 kenan tun da wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sace 'yan makarantar a garin Chibok.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.