BBC navigation

Cutar numfashi ta kashe mutane 102 a Saudiyya

An sabunta: 28 ga Aprilu, 2014 - An wallafa a 13:00 GMT

Alamomin cutar sun hada da zazzabi da mura mai zafi da kuma cutar koda

Cutar numfashi da ke saurin kisa ta Mers ta kashe fiye da mutane 100 a Saudiyya, tun bayan bullarta a kasar a shekarar 2012.

Hukumomin lafiya na kasar sun ce wasu karin mutane takwas sun mutu a ranar Lahadin da ta wuce, hakan ya kawo adadin zuwa 102.

Yawan mutanen da suka kamu da cutar na karuwa, yayin da hukumar lafiya ta duniya WHO, ta nemi taimaka wa kasar ta hanyar binciken yadda ake kamuwa da cutar.

A ranar Asabar ne aka samu mutum na farko, wani mai shekaru 27 da ya kamu da cutar a Masar, bayan ya dawo daga Saudiyya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.