Gwamnatin Birtaniya ta cire hannu a BBC

  • 1 Aprilu 2014
Aicchatou Mousa ta sashen Hausa na BBC
Koma wa dogaro da haraji ne yasa aka hade wasu shirye-shiryen BBC na turanci

Daga ranar Talata ne gwamnatin Burtaniya za ta tsame hannuwanta daga samar da kudaden gudanar da sashen Hausa na BBC.

Hakan ya shafi duka sauran sassa masu watsa shirye-shirye ga kasashen waje, wato BBC World Sevice.

Abin da ke nufin za a rika amfani da harajin da masu kallon talabijin a Burtaniya ke biya, wajen gudanar da sassan.

Editan sashen Afrika na BBC Solomon Mugera ya ce, koma wa dogaro da harajin ne yasa aka rufe wasu sassa na harsunan kasashen waje, kuma aka zaftare kudaden kasafin kudaden sassan da ke cigaba da aiki.