Paparoma Francis ya gana da Obama

  • 27 Maris 2014
Paparoma da Obama a fadar Vatican

Paparoma Francis ya yi ganawarsa ta farko da shugaban Amurka, Barack Obama.

Tattaunawar a fadar Vatican, ta soma ta ne inda Shugaban Amurkar ya bayyana kan sa a matsayin babban wanda Paparoman yake burgewa.

A bainar maneman labarai da masu daukar hotuna dukkaninsu sun yi murmushi kuma suka yi masabiha.

Mr Obama ya shaidawa wata jaridar Italiya cewar yana kallon Paparoma a matsayin wanda ke kokarin rage tazarar dake tsakanin masu kudi da matalauta amma dai suna bambamcin ra'ayi a kan wasu bututuwan.

Batun cire ciki da kayyade iyali da kuma auren jinsi guda su ne batutuwan da suka sha bambam a kai.