BBC navigation

Kashe na'urar jirgin Malaysia aka yi

An sabunta: 15 ga Maris, 2014 - An wallafa a 07:11 GMT

Jirgin da ya bace sama da kwanaki bakwai har yanzu ba duriyar sa

Pirai Ministan Malaysia ya ce da gangan aka kashe na'urar sadarwar jirgin kasar, wanda ya bace a makon jiya dauke da mutane 239.

Mr Najib Razak ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gudanar da safiyar Asabar, inda ya ce sun fahimci kaguwar da jama'a suka yi na samun bayani game da 'yan uwansu.

Ya kuma tabbatar da cewa yanzu akalar binciken ta karkata zuwa ga tekun India bayan da alamu ke nuna cewa an karkata akalar jirgin.

Sai dai bai tabbatar da rahoton da wani jami'in gwamnatinsa ya bayyana cewa fashin jirgin aka yi ba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.