An dawo da layukan sadarwa a jihar Borno

  • 13 Maris 2014
Jamian sojin Najeriya
Jamian sojin Najeriya

Rahotani da daga Maiduguri sun ce an dawo da layukan sadarwa a wasu sassa na jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

A jiya ne dai mahukuntan kasar suka bayana cewa sun sake dakatar da layukan sadarwa a jihar Borno saboda fadan da suke yi da masu tada kayar baya ya yi tasiri.

Kamfanin dilanci labaru na AFP ya ambato kakakin rundunar tsaro ta hadin gwiwa kanar Muhamadu Dole na cewa sun dau matakin ne sakamakon ayyukansu na baya baya nan akan sansanonin kungiyar da ake kira boko haram.