Jami'in Majalisar dinkin duniya ya soki majalisar

  • 2 Maris 2014
Jami'in ya kuma bukaci a hukunta sojojin majalisar

Wani babban jami'in Majalisar dinkin duniya ya raba gari da majalisar inda ya fito fili ya bukaci da a biya mutanen da annobar cutar amai da gudawa ta shafa a Haiti daga 2010 wadda ta kashe sama da mutane dubu takwas.

Mutumin wanda shi ne babban jami'in kare hakkin dan adam na Majalisar a Haiti, Gustavo Gallon ya bukaci da a biya wadanda annobar ta shafa diyya tare da hukunta wadanda ke da alhakin yada cutar.

Bincike ya nuna sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya daga Nepal ne suka zubar da dagwalon bahaya da ke dauke da kwayoyin cutar a kusa da wani kogi, lamarin da ya yi sanadiyyar yada cutar ta kwalara.

Amma kuma sashen shari'a na Majalisar ya ce sojojin suna da kariyar diflomasiyya.