BBC navigation

An yanke wa Adebolajo da Adebowale hukunci

An sabunta: 26 ga Fabrairu, 2014 - An wallafa a 18:52 GMT

Mutanen biyu a lokacin da lamarin ya faru

An yankewa masu tsatsauran ra'ayin musuluncin nan biyu da aka tuhuma da kisan sojan Birtaniya, Lee Rigby a nan London bara hukuncin ɗaurin rai da rai.

Michael Adebolajo da Michael Adebowale sun kaɗe soja Lee Rigby ne da mota, kana suka auka masa da sara, lamarin da ya firgita jama'a sosai.

Mutanen biyu wadanda shiga musulunci suka yi, an yanke musu hukunci ne a bayan idonsu bayan an samu wata jayayya da jami'an tsaro a kotu.

Shi dai Adebolajo ya yi ikirarin cewa, "shi sojan Allah ne" , kuma ya ce, kisan sojan da suka aikata tamkar wani yaki.

An yankewa Micheal Adebolajo hukuncin zama a gidan maza har iyakar ransa, amma shi Micheal Adebowale zai yi zaman gidan kaso na tsawon shekaru akalla 45.

Su dai mutanen biyu sun kashe Lee Rigby ne a unguwar Woolwich dake kudu maso gabashin London.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.