BBC navigation

An kashe wani kwamanda a Syria

An sabunta: 24 ga Fabrairu, 2014 - An wallafa a 01:47 GMT

Ana kara samun rashin jituwa tsakanin 'yan gwagwarmayar Islama a Syria

Masu fafutuka a Syria sun ce an kashe wani babban kwamandan 'yan tawaye da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda a wani harin kunar bakin wake.

Kwamandan kungiyar 'yan gwagwarmayar Islaman mai suna Abu Khaled al-Suri na daga cikin mutane da yawa da aka kashe.

Lokacin da wasu 'yan gwagwarmayar masu adawa da kungiyarsa suka kai farmaki sansanin kungiyar tasa, me suna Ahrar Al-Sham a Aleppo.

Magoya bayan kwamandan sun zargi wata kungiyar ta 'yan gwagwarmaya me suna ISIS a takaice da hannu a kisan shi, amma kungiyar ta musanta hakan.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.