'Wasan Hutton a Aston villa yazo karshe'

  • 21 Fabrairu 2014
Hutton yana wasa
Aston villla na fuskantar matsalolin kudi

Da wuya dan wasan bayan Kulab din Aston Villa Alan Hutton ya sake taka wasa a kulab din saboda matsalolin kudi da kulab din ke fuskanta kamar yadda Manajan kulab din Paul Lambert ya bayyana.

Dan wasan mai shekaru 29 a duniya wanda ake biyansa £40,000 a mako kamar yadda rahotanni suka nuna, bai takawa Villa was aba tun watan Mayun shekarar 2012.

Da aka tambaye shi idan Hutton zai sake takawa Villa wasa, Lambert y ace “ Zai yi wuya” Ya san da haka.

Hutton wanda kwanturaginsa zai kare a shekarar 2015 ya tafi zuwa Nottinghma a matsayin aro a watan Disambar shekara 2012