An kama 'yan Arewa 400 a Bayelsa

  • 11 Fabrairu 2014
Taswirar Jihar Bayelsa a Najeriya
Taswirar Jihar Bayelsa a Najeriya

Jami'an hukumar shige da fice a Najeriya sun kama wasu 'yan arewacin kasar mazauna jihar Bayelsa 400 a Yenagoa babban birnin jihar.

Kamen wanda hukumar ta kaddamar ranar Litinin, ta ce wani mataki ne da ta kan dauka a duk fadin kasar don tantance bakin haure.

Sai dai wannnan al'amari ya zo ne a dai-dai lokacin da ake yawan kama 'yan asalin arewacin Najeriya, bisa zarginsu da kasancewa wata barazana ta fuskar tsaro ko ma 'yan kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah lid Da'awati wal jihad, wadda aka fi sani da suna Boko Haram.

Wani dan arewacin Najeriyar mazaunin Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa ya ce mutanen da aka cafke masu kananan sana'oi ne da suka jima suna harkokinsu a jihar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar shige da ficen ya tabbatar da kamen amma bayan tantancewa har an saki mutane 100 daga cikin su.

Cikin wadanda hukumar ta saka kuwa har da 'yan asalin Jamhuriyar Nijar masu cikakkun takardun zama a Najeriya.