BBC navigation

Boko Haram: Mutane 40,000 sun tsallaka Niger

An sabunta: 10 ga Fabrairu, 2014 - An wallafa a 16:11 GMT

Wadanda suka gujewa rikicin Boko Haram

Hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce kawo yanzu mutane 40,000 ne su ka gujewa rikicin Boko Haram a Nigeria su ka tsallaka zuwa makwabciyar kasar Niger.

Jami'in hukumar a Jamhuriyar Niger wanda ya bayyanawa BBC hakan, ya ce za su tallafawa dubban 'yan gudun hijirar musamman wanda ke zaune a yankin Diffa.

A yanzu haka dai jami'an hukumar ta majalisar dinkin duniya da na gwamnatin Niger su na ziyarar gani da ido a jihar ta Diffa don tattance irin tallafin da za a baiwa mutanen

Abubakar Shekau na Boko Haram

Mutanen da suka tsallaka sun hada da 'yan Nigeria da 'yan Niger da kuma 'yan Chadi.

Mutanen wadanda suke cikin mawuyacin hali sun yada zango ne a garuruwan Geskerou, Diffa, Toumour, Nguelkolo da kuma Chetimari.

'Tallafin Red Cross'

Sakamakon yanayi marar dadin da 'yan gudun hijirar ke ciki, kungiyar agaji ta Red Cross a Jamhuriyar Niger, ta ce daga watan Mayun 2012 zuwa yanzu ta bada tallafi ga dubban mutanen da suka gujewa yakin.

Sojojin Nigeria na sintiri a cikin birnin Maiduguri

Kakakin kungiyar Oumarou Daddy Rabiou ya shaidawa BBC cewar "Yawancinsu mata ne da kananan yara, sannan kuma akwai 'yan Niger da Nigeria da kuma 'yan Chadi a cikin 'yan gudun hijirar".

Rikicin Boko Haram musamman a arewa maso gabashin Nigeria ya janyo rasuwar daruruwan mutane tare da barnata dukiya ta miliyoyin kudi.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa a kokarin kawo karshen zubar da jinin da ake yi.

Sai dai rahotanni sun nuna cewar duk da irin matakan da gwamnati ta ce ta na dauka don kawo zaman lafiya, har yanzu 'yan Boko Haram na samun damar kai hare-hare a yankin.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.