'Jonathan ya sallami shugaban ma'aikatansa'

  • 10 Fabrairu 2014
Ana zargin an sallami Oghiadomhe ne saboda yana da hannu a wata cuwa-cuwa

Fadar gwamnatin Najeriya ta ce shugaban ma'aikatan Shugaba Goodluck Jonathan ya yi murabus don ya samu damar tsayawa takara a zabuka masu zuwa.

Wata sanarwa ce daga mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Reuben Abati, ta bayyana cewa Mike Oghiadomhe ya ajiye aikinsa saboda yana da burin shiga siyasa.

Sai dai kuma wadansu majiyoyi a fadar gwamnatin sun ce sallamar shugaban ma'aikatan aka yi.

Wadansu rahotanni dai na zargin cewa an sallami Mista Oghiadomhe ne saboda zargin da ake yi cewa yana da hannu a wata cuwa-cuwa a kamfanin man kasar, wato NNPC.

Ana ganin Mike Oghiadome na cikin mutane na kusa-kusa ga shugaban kasar.