BBC navigation

An nemi a kafa hukumar sayar da dabbobi

An sabunta: 31 ga Janairu, 2014 - An wallafa a 06:54 GMT

ana satar dabbobi zuwa kudanacin Najeriya

Kungiyoyin Fulani da masu sayan dabbobi a Najeriya sun nemi a kafa wata hukumar tantance sayar da dabbobi a kasar.

Kungiyoyin sun bayyana hakan ne a sakamakon yadda suka ce ake shigo da dabbobin sata daga arewa zuwa babbar mayankar dabbobi ta kasa dake Agege a Jihar Lagos .

Daukar wannan mataki dai ya zo bayan kwamitin kasuwar mayankar dabbobin ta kama motar titiri cike da shanun da ta ce na sata ne daga arewacin kasar.

Harkar safarar dabbobi daga arewacin kasar zuwa kudanci abune da aka jima anayi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.