Mutane 2,000 a Kawuri na neman mafaka

  • 31 Janairu 2014
Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Hukumar agajin gaggawa ta Nigeria- NEMA ta ce mutane fiye da 2,000 ne suka rasa mutsugunansu a jihar Borno sakamakon harin da aka kai a kauyen Kawuri dake karamar hukumar Konduga.

A cewar NEMA din, harin da aka kai a kasuwar kauyen da kuma kona gidajen jama'a ya shafin mutane fiye da 4,000.

Harin da aka kai na kauyen Kawuri a ranar Lahadin da ta wuce, ya janyo rasuwar mutane fiye da 83 tare da hasarar dukiyoyi da dama.

A cikin wannan makon ne Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya kai ziyara kauyen don ganin irin barnar da aka yi, kuma ya dauki alkawarin tallafawa mutanen da lamarin ya shafa.

Kungiyar Boko Haram wacce cibiyar ta ke jihar Borno, ta janyo mutuwar daruruwan mutane a hare-haren da ta kai a cikin shekarun ukun da su ka wuce.