BBC navigation

An amince a sake shari'ar soji a Turkiyya

An sabunta: 6 ga Janairu, 2014 - An wallafa a 07:34 GMT

Akwai yiuwawar a sake shari'ar sojojin da aka tuhuma da hmbara da mulkin Erdogan

Pirai ministan Turkey Recep Tayyep Erdogan ya amince a sake shari'a ga jami'an soji da a baya aka zarga da hambarar da mulkinsa.

A baya dai babban mai ba shi shawara ya ce 'yan sanda da masu shigar da kara sun shiryawa jami'an sojin gadar zare.

A watan Disambar bara ne masu shigar da karar suka sa aka kame wasu daga cikin abokan Mr Erdogan da aka tuhume su da laifin cin hanci da rashawa.

Wakilin BBC a birnin Santambul ya ce wannan sabon jawabi na Mr Erdogan ya nuna cewa a yanzu ya na goyon bayan bangaren sojojin kasar masu raba siyasa da addini wadanda yake adawa da su a baya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.