BBC navigation

'Amurka ce babbar barazana a duniya'

An sabunta: 30 ga Disamba, 2013 - An wallafa a 11:48 GMT

Binciken ya nuna cewa sai an fi samun zaman lafiya da a ce akasarin mata 'yan siyasa ne

Wani bincike ya nuna cewa kashi daya bisa hudu na mutanen duniya sun yi ammanar cewa Amurka ce babbar barazana wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Sai dai binciken, wanda da kungiyar WIN/Gallup International ta gudanar, ya kara da cewa Amurka ce kasar da ta fi shahara, inda mutane ke koma wa da zama.

Kazalika kungiyar ta ce mutanen da ta yi wa tambayoyi lokacin binciken sun bayyana cewa suna fatan shekarar 2014 za ta fi shekarar 2013 armashi.

Haka kuma sun ce za a fi samun zaman lafiya a duniya da a ce akasarin mata 'yan siyasa ne.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.