BBC navigation

Dakarun Machar na jerin gwano a garin Bor

An sabunta: 28 ga Disamba, 2013 - An wallafa a 20:17 GMT
Riek Machar

Riek Machar

A Sudan ta kudu dubban matasa magoya bayan jagoran 'yan tawaye Riek Mashar suna tunkarar garin Bor, mai matukar muhimmanci, wanda kuma shi ne babban birnin jihar Jonglei.

Yanzu haka dai dakarun gwamnati ne suke iko da garin na Bor, bayan sun kwace shi daga 'yan tawaye da tun farko suka kwace garin yayin da ake cigaba da fadan kabilanci a kasar.

Gungun matasan dai wani bangare ne na sojan sa kai 'yan kabilar Nuer.

Kuma kakakin shugaban kasar, Ateny Wek Ateng ya musanta cewa gwamnati tana shirin kai hari a garin Bentiu.
Dakarun 'yan tawaye ne suka aukawa garin bayan jagoransu Riek Mashar ya yi watsi da tayin zaman lafiya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.