BBC navigation

Rikici ya barke a jam'iyyar APC

An sabunta: 19 ga Disamba, 2013 - An wallafa a 09:11 GMT

Shugaban riko na jam'iyyar APC, Bisi Akande.

Rikici ya barke a babbar jam'iyyar adawa ta Nigeria, APC, bayan da wasu 'ya'yan jam'iyyar suka yi zargin cewa ana fifita gwamnoni biyar da suka shigo daga PDP kan wadanda suka tarar a ciki.

A jihar Sokoto, bangarorin tsohuwar jam'iyyar ANPP da CPC da kuma bangaren sabuwar PDP duk sun bude ofisoshi mabambanta inda su ke ikirarin su ne halatattun masu jam'iyyar.

A jihar Adamawa, 'yan takarar gwamna a zaben 2011 karkashin tsofaffin jam'iyyun CPC da ACN, Birgediya Buba Marwa da Cif Marcus Gundiri sun ce ba su amince gwamna Murtala Nyako ya zama jagoran jam'iyyar ba.

A jihar Kano kuwa, tsohon gwamna Ibrahim Shekarau ne ya jagoranci 'yan tsohuwar jam'iyyar ANPP zuwa hedikwatar APC dake Abuja bisa korafin cewa ba su amince gwamna Rabiu Kwankwaso ya jagoranci jam'iyyar ba.

Shigowar gwamnonin PDP na haddasa rikici a APC

Masu korafin dai su na cewa su ne suka kafa jam'iyyar APC don haka bai kyautu wasu baki su zo su girbi abin da ba su shuka ba.

Su kuma magoya bayan gwamnonin biyar cewa su ke wanda ya fi jama'a shi yafi dacewa da jagoranci kuma tsarin mulkin jam'iyyar APC ya tanadi cewa gwamnoni su ne jagororin jam'iyyar a jihohinsu.

Kawo yanzu dai shugabannin jam'iyyar ta APC ba su baiyana matsayinsu game da wannan takaddama ba.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.