BBC navigation

An aurar da mata fiye da 1000 a Kano

An sabunta: 19 ga Disamba, 2013 - An wallafa a 17:27 GMT

Gwamnatin Kano ta ce ta bullo da shirin ne domin rage matsalolin da suka shafi iyali.

Gwamnatin jihar Kano da ke Nigeria ta aurar da mata 1111 a karkashin tsarin auren da hukumar Hizba ta jihar ke shiryawa.

Cikin wadanda aka daura wa auren har da zawarawa da mabiya addinin Kirista da masu fama da cutar HIV.

Wannan ne dai karo na hudu da hukumar ke shirya irin wannan aure da nufin rage yawan zawarawa da kuma magance yawaitar mutuwar aure.

Gwamnatin Kano da 'yan kasuwa da kuma wasu kamfanoni ne dai ke daukar dawainiyar angwayen da amare.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.