Za a nemi taimako don mutanen Syria

  • 16 Disamba 2013
Yan gudun hijira na Syria
Za a nemi taimako don mutanen Syria

Majalisar Dinkin Duniya tana shirin kaddamar da asusun neman taimako mafi girma ranar Litinin, wanda mafi rinjayen abin da zai tara za a mika su ne ga miliyoyin mutanen da yaki ya shafa a kasar Syria.

Wani sabon nazari da kwamitin ceto na duniya ya gudanar ya ce dukkan hudu daga cikin mutane biyar 'yan kasar Syria suna cikin damuwa cewar abincinsu zai kaare.

Yace, a wasu sassan kasar Syria, farashin burudi ya ninka har sau biyar farashin da ake sayar da shi shekaru biyu da suka gabata.

Babbar jami'ar hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta gaya ma BBC cewar 'yan gudun hijirar na Syria suna ganin duniya ba ta fahimci halin kuncin da suke ciki ba, shi yasa suka gaza wani yunkuri na taimaka musu.

Karin bayani