BBC navigation

Ana bikin binne Nelson Mandela a Qunu

An sabunta: 15 ga Disamba, 2013 - An wallafa a 07:40 GMT

Ana shirin binne Nelson Mandela

A yau Lahadi ne za a binne tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela a garin da ya taso; Qunu wanda yake a gabashin Cape, bayan an yi jana'izarsa.

Jana'izar tasa dai za ta kunshi al'adu na hukuma da kuma tsatsibe tsatsibe na kabilarsu , da ya hada da yanka wani bijimin sa.

Kimanin baki dubu biyar ne (5,000) ne za su yi wa gawar ban girma na karshe a bikin da za a yi a wata makekiyar rumfa fara da aka kafa a kauyen.

Sai dai kuma mutane 400 ne kawai da suka hada da matarsa Graca Machel da shugaban kasar na yanzu Jacob Zuma za su je wajen kabarinsa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.