Cutar amai da gudawa ta barke a Kano

Ana cin kwayar cutar ne ta baki, ta hanyar cin kayan lambu ko ganyayyakin da ba a tsaftace ba

Hukumomin lafiya a jihar Kano dake arewacin Nigeria sun tabbatar da mutuwar sama da mutane goma sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a cikin birnin.

Lamarin dai ya fara ne tun karshen makon jiya, inda kawo yanzu ake ci gaba da kai mutane asibitoci.

A yanzu dai mazauna wasu unguwanni na birnin Kano da matsalar ta amai da gudawa ta fi kamari na cikin zullumi, ganin yadda nan da nan cutar ke lahanta duk wanda ya hadu da ita, inda har wasu ma ke rasa rayukan su sabo da cutar.

Kawo yanzu dai saboda yawan masu kamuwa da cutar asibitin zana da ake garzayawa da wadanda suka kamu ya cika, abinda ya sa ke nan hukumomi suka ce sun gama shirin bude wasu asibitocin, musamman a sassan da lamarin ya fi kamari.

Masana kiwon lafiya dai sun ce ana cin kwayar cutar ne ta baki, idan aka yi amfani da lambu ko ganyayyaki da ba a tsaftace ba, ko kuma mutum ya taba kwayar cutar da hannun sa, sannan ya ci abinci da hannun ba tare da ya wanke sosai ba.