BBC navigation

An fara bikin 'yancin kai a Kenya

An sabunta: 12 ga Disamba, 2013 - An wallafa a 02:54 GMT
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta

Shugaba Uhuru Kenyatta wanda a wannan ranar mahaifinsa Jomo ya kasance shugaban kasar na mulkin kai na farko, shi ne ya jagoranci bikin.

Al'ummar kasar Kenya sun fara bukukuwan mako guda na zagayowar ranar samun 'yancin kan kasar daga Birtania, tsohuwar uwar gijiyarta ta mulkin mallaka.

An gudanar da wani biki a lambun Uhuru da ke babban birnin kasar, Nairobi.

Inda aka sauke tutar Birtaniya tare da daga tutar Kenya, kamar dai yadda aka yi a wurin ranar 12 ga watan Disamba na 1963.

Hakan na nuna samun 'yancin kan kasar daga Birtaniya.

Cuncurundon al'ummar kasar sanye da tufafi masu launin tutar kasar sun rika kada tutar kasar, sannan kuma an yi wasan wuta a dandalin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.