BBC navigation

Takunkumin Iran na nan daram - Kerry

An sabunta: 5 ga Disamba, 2013 - An wallafa a 15:47 GMT
John Kerry da Benjamin Netanyahu

Tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinu ta gagara karewa shekara da shekaru

Sakataren harkokin wajen Amurka ya bai wa Fraiministan Isra'ila tabbacin cewa ba za a cire wa Iran manyan takunkumin da aka sa mata ba.

John Kerry ya tabbatar wa Benjamin Netanyahu duk da yarjejeniyar da aka kulla da Iran din ta wucin-gadi akan shrinta na nukiliya muhimman takunkumin na nan.

Bayan wata tattaunawa da Netanyahu a birnin Kudus, Mr Kerry ya ce tsaron Isra'ila shi ne babban abin da Amurka ta sa a gaba a yankin.

Mr Kerry ya je Kudus ne domin wanzar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.