BBC navigation

Allah ya yi wa Nelson Mandela rasuwa

An sabunta: 5 ga Disamba, 2013 - An wallafa a 23:06 GMT

Mandela shi ne bakar fata na farko da ya shugabanci Afrika ta Kudu

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela ya rasu. Gwamnatin Afrika ta Kudu ce ta bayar da sanarwar mutuwar a daren ranar Alhamis.

Nelson Mandela wanda a shekara ta 1994, ya zama shugaban Afrika ta Kudu bakar fata na farko, ya dade yana fama da laulayi, ga kuma yawan shekaru.

An daure shi ne bisa laifin hada baki domin hambarar da gwamnatin farar fata 'yan tsiraru ta mulkin wariyar launin fata.

Shugaba Mandela dai yana da tarihi na rashin lafiyar huhu, tun daga lokacin da ya kamu da cutar tarin fuka a gidan kurkuku.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.