BBC navigation

An kashe mutane tara a Libya

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2013 - An wallafa a 13:06 GMT
Tashin hankali a Benghazi

Fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan gawagwarmaya masu kishin Islama ya zama jiki a Benghazi

An yi mummunan dauki ba dadi tsakanin dakarun gwamnati da kuma mayaka masu tsattsauran kishin Islama a Beghazi da ke gabashin Libya.

An kashe akalla mutane tara wasu hamsin kuma sun samu raunuka a fadan da aka fafata tsawon sa'oi.

Jami'an tsaro sun ce fadan ya barke ne lokacin da aka kai hari kan wani mutum farar hula a wani wurin binciken ababan hawa na masu kishin Islaman, Ansar al-Sharia.

Ana ganin fadan a matsayin sa-in-sa mafi muni tsakanin dakarun gwamnati da kungiyar 'yan gwagwarmayar.

Ana dora alhakin kisan alkalai da jami'an tsaro da dama akan wannan rashin jituwa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.