An tsare 'yan Nigeria 53 a India

  • 1 Nuwamba 2013
Manmohan SIngh, Praministan India

Jami'an tsaro a jihar Goa ta India sun tsare 'yan Najeriya su 53 bayan wani gungun 'yan Najeriya su kusan 200 sun rufe wata babbar hanya tsawon kusan awa hudu.

'Yan Najeriyar da aka kama dai suna nuna rashin jin dadinsu ne saboda kisan wani dan Najeriyar da a wani lamari da ake zargin yana da alaka da hada-hadar muggan kwayoyi.

Dan Najeriyar da aka kashe mai suna Obina Paul Obiwesi an samu gawarsa ce a kauyen Parra dake kusa da gabar teku inda yayi kaurin suna wajen harkar muggan kwayoyi.

'Yan Najeriyar dai sun rufe hanyar ce, suna zargin cewa ana yi musu bita da kulli a yankin.

Kafin dai a kawo karshen lamarin sai da aka yiwa wasu 'yan Najeriya biyu mummunan duka har sai da aka kwantar da su a asibitin Goa.