BBC navigation

Wani Fasto ya sayar da jaririyar 'yarsa a Najeriya

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2013 - An wallafa a 20:40 GMT
Mohammed Abubakar

Mohammed Abubakar, Sufeta Janar na Yansandan Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Imo a Najeriya ta damke wani Fasto da wani likita da wata mata, bisa zargin sayar da wata jaririya wadda 'yar Faston ta haifa hakanan ba tare da tayi aure ba.

Yayin da 'yar Faston ke kukan a kawo mata 'yarta, har yanzu ba a san yadda aka yi da jaririyar ba.

A yau rundunar 'yan sandan ta nuna wadannan mutane ga manema labarai.

Batun safarar jarirai dai na ci gaba da zama wata babbar matsala, tare da daukar sabon salo a shiyyar kudu maso gabashin Najeriyar

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.