BBC navigation

Nazari kan hakkin bil'adama a Najeriya

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2013 - An wallafa a 12:00 GMT
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya

Najeriya ita ma za ta gabatar da ayyukanta a tsawon wannan shekaru

Majalisar Dinkin Duniya za ta yi bibiyar ayyukan hukumar kare hakkin bil'adama ta Najeriya, na tsawon shekaru hudu.

A zaman Majalisar wanda ake yi a Geneva, kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International za ta gabatar da nata rahoton, game ayyukan kare hakkin bil'adama a Najeriyar.

Rahoton Amnesty zai tabo batutuwan da suka hada da Boko Haram da kisan gillar da ake zargin jami'an tsaro da aikata wa da matsalar malalar mai dake janyo gurbata muhalli a Niger Delta da hukuncin kisa da kuma auren jinsi.

A cewar Amnesty Najeriya ba ta yi wani abin a zo a gani ba, wajen aiwatar da shawarwarin inganta hakkin dan adam da aka bata a shekarar 2009.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.