'Yan sanda sun hana zabe a Maldives

  • 19 Oktoba 2013
zabe a Maldives
zabe a Maldives

'Yan sanda a kasar Maldives sun hana kada kuri'a a zaben shugaban kasa jim kadan bayanda hukumar zabe ta bayyana shirin gudanar da zaben.

Shugaban hukumar zaben Fuwad Thowfeek yace 'yan sanda sun mamaye hukumar, tare da hana jami'ai gudanar da ayyukansu.

'Yan sandan sun ce zaben ya sabawa umarnin kotun kolin kasar.

A makon jiya ne dai kotun ta soke sakamakon zagaye na farko na zaben bisa zargin tafka magudi.

Jagoran 'yan adawa Muhammad Nasheed ne ya lashe kaso arba'in da biyar cikin dari na kuri'un da aka kada yayinda shugaba mai ci, Muhammad Waheed ya samu kaso biyar kacal.