BBC navigation

Fada ya barke a Mali

An sabunta: 29 ga Satumba, 2013 - An wallafa a 20:28 GMT
sojan Mali a garin Kidal

Fadan ya kawo cikas ga shirin dakatar da bude wuta da sabuwar gwamnatin ta sa a gaba

Fada ya barke a garin Kidal na arewacin Mali inda ake zargin mayakan Abzinawa da kai hari kan sojin gwamnati.

An ruwaito gwamnan lardin, Adama Kamissoko yana cewa ana ta musayar wuta a garin na Kidal.

Kwanaki uku da suka wuce 'yan awaren sun ba da sanarwar za su kawo karshen tsagaita wutar da suka yi da sabon shugaban kasar Malin Ibrahim Boubakar Keita.

wanda ya sha alwashin ba da fifiko kan harkokin tsaro.

Ranar Asabar an kai wani harin kunar-bakin-wake a mota a kofar wani sansanin soja a birnin Timbuktu.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.