BBC navigation

An yi wa mutum dashen hanci a goshi

An sabunta: 26 ga Satumba, 2013 - An wallafa a 16:22 GMT
Xiaolians kenan da sabon hancinsa a goshi

Xiaolians kenan da sabon hancinsa a goshi

Likitoci sun dasa hanci a goshin wani mutum da zummar cire shi idan ya yi toho don sanya shi a hancinsa wanda ya zaizaye bayan wani hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Mutumin maisuna Xiaolian, dan shakeru 22, bai kula da hancin nasa da ya lalace ba bayan hatsarin da ya yi a watan Agustan 2012, lamarin da ya sanya hancin ya zaizaye ta yadda likitoci ba za su iya mayar da shi ba.

Hakan ne ya sanya suka dasa masa wani hancin a goshinsa a asibitin Fuzhou da ke lardin Fujian na kasar China.

Likitoci sun ce sabon hancin nasa yana da kyau, kuma nan ba da dadewa ba ne za a yi masa tiyata domin dasa masa shi.

Mista Shehan shi ne shugaban likitocin da za su yi wa Xiaolian tiyata, kuma ya ce a goshi ne kawai za a samu fatar da za ta iya sanya hanci ya yi tsuro.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.