Ina nan a raye- Abubakar Shekau

  • 25 Satumba 2013
Abubakar Shekau

Shugaban Kungiyar Jama'atu AhlusSunnah Lidd'awati wal Jihad wato Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon bidiyo inda ya ce yana nan da rai.

A sakon wanda BBC ta samu sautinsa, Shekau ya ce kungiyarsa ce keda alhakin kashe mutane a BeniSheik da Monguno a jihar Borno.

Kuma a cewarsa, mutane kusan 200 ne suka mutu sabanin adadin mutane kusan 160 da jami'ai suka ce sun hallaka sakamakon harin.

Abubakar Shekau a cikin sakon wanda mabiyansa ke kabbara, ya ce babu gudu babu jada baya a kokarinsu na tabbatar da addinin musulunci tare da yaki da mulkin demokradiyya.

A watan Agusta ne, Rundunar hadin gwiwa ta tabbatar da tsaro a jihar Borno-JTF ta fitar da wata sanarwa inda tace watakila, Abubakar Shekau ya mutu sakamakon harbin bindiga a bata kashi da jami'an tsaro.

Karin bayani