BBC navigation

Ana ci gaba da fafatawa a Kenya

An sabunta: 23 ga Satumba, 2013 - An wallafa a 18:39 GMT
Harin Alshabab a Nairobi

Sojoji sun ce an kubutar da mafi yawan mutanen da aka yi garkuwa da su

Rahotanni daga Nairobi babban birnin Kenya sun bayyana cewa ana ci gaba da fafatawa tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindigar da suka yi garkuwa da mutane a rukunin kantunan Westgate.

Wuta na ci gaba da ruruwa a ginin, inda hayaki ya mamaye sararin samaniyar yankin.

Ministan harkokin cikin gida na kasar, Joseph Ole Lenku, ya shaidawa BBC cewa an kusa kawo karshen abin da ya kira matsalar da ake fuskanta.

Ya kara da cewa dakarun kasar sun kwace iko da dukkan benayen da ke cikin ginin.

Rahotanni na cewa an kashe akalla 'yan bindiga guda uku, kana aka ji wa wasu rauni.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.