BBC navigation

2020: Australia za ta nemi diyya

An sabunta: 17 ga Satumba, 2013 - An wallafa a 16:34 GMT
Firai ministan Australia, Tony Abbott

Kasashen Australia da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Amurka ne suka nemi bakuncin gasar, amma ba a zabe su ba

Shugaban hukumar kwallon kafa na Australiya, Frank Lowy yace watakila kasar ta nemi diyya, idan an sauya lokacin gasar cin kofin duniya zuwa hunturu.

Austaraliya ba ta samu nasarar daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na 2022 ba, duk da cewa ta kashe kimani fam miliyon 25.

Qatar ce ta samu nasarar daukar bakuncin gasar daga cikin kasashe hudu da suka nemi bakuncin gasar, amma a yanzu hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA na tunanin sauya lokacin gasar zuwa hunturu.

Yanayi zafi a Qatar na kaiwa ma'aunin Celsius 50 a watan Yuni da Yuli, abin da ya sa FIFA ke tunanin yin gasar a lokacin bazara a karo na farko a tarihin gasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.