BBC navigation

Mutuwar yara bai ragu ba a Najeriya - UNICEF

An sabunta: 13 ga Satumba, 2013 - An wallafa a 14:25 GMT
Tambarin asusun UNICEF

Rahoton an fitar da shi ne da hadin gwiwar babbn bankin Duniya da kuma hukumar lafiya ta duniya

Wani rahoto da asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya, UNICef ya fitar a ranar juma'a, game da mace-macen kananan yara ya ragu zuwa rabi daga shekarar 1990.

Sai dai kimanin yara sama da miliyan shida ne suka mutu a bara, kuma kusan rabinsu sun fito ne daga kasashe biyar wato Najeriya da Congo da India da Pakistan da kuma China.

Abin da ke nufin akwai bukatar kasashe irinsu Najeriya su kara shan damara, wajen magance matsalar.

Rahoton yace ba a samu wani sauyi ba game da yawan yara 'yan kasa da shekaru biyar, dake mutuwa a tsakiya da yammacin Afrika.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.