BBC navigation

Shugabannin China da Japan sun yi musabaha

An sabunta: 6 ga Satumba, 2013 - An wallafa a 05:15 GMT

Shinzo Abe yana marhabin da wata tawagar majalisar dokokin Amurka a birnin Tokyo.

A wani lamarin da ya zo da ba-zata, shugabannin kasashen China da Japan sun yi musabaha sun kuma yi magana da juna a wurin taron koli na kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da ake yi a St Petersburg.

Wani jami'in gwamnatin Japan ya ce, Farayin ministan Japan Shinzo Abe da Shugaban kasar China Xi Jinping sun gana har tsawon kimanin mintuna biyar, sun kuma yi magana ta hanyar tafinta.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu wadda ta yi rauni tun shekaru da dama, ta kara tabarbarewa sakamakon ikirarin da dukkansu ke yi na mallakar wasu kananan tsibirrai dake gabashin tekun China.

Wannan dai shi ne karon farko na haduwar shugabannin biyu tun bayan da suka kama ragamar mulki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.