BBC navigation

An harbe wani jariri a New york

An sabunta: 3 ga Satumba, 2013 - An wallafa a 08:37 GMT

Mutane dai sun fara zuwa unguwar da lamarin ya faru domin yin ta'aziyya.

'Yan sandan birnin New York na Amurka sun shiga farautar wani dan bindiga, da ya harbe wani jaririn da ke ciki wani keken yara.

An harbi yaron mai shekara daya ne a gefen kansa, a yankin karamar hukumar Brooklyn.

Kwamishinan 'yansanda, Raymond Kelly ya ce ya yi amanna cewa mahaifin yaron aka hara, wanda shi ne ke tura keken jaririn a kan titi, kuma lamarin na da alaka da harkar kungiyoyin 'yan daba.

Magajin garin New York Michael Bloomberg, ya ce kisan wani babban abin fargaba ne ga iyayen yaron, da al'ummar yankin na Brookyn da ma birnin ga baki daya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.