Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da sojoji

  • 27 Agusta 2013

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarunta na tabbatar da zaman lafiya hudu sun bace a yankin Darfur na Sudan bayan da ambaliyar ruwa ta tafi dasu.

Jami'ar Majalisar, Rania AbdulRahman ta ce dakarun sun yi wa wata tawaga rakiya lokaci da ruwa mai karfi ya yi ayon gaba dasu.

Sai dai ta ce wasu dakarun biyu sun tsira bayan da masu aikan agajin suka cecesu.

Ambaliyar ruwa ta shafi mutane fiye da 300,000 a fadin kasar Sudan inda mutane fiye da 50 suka rasu a watan Agusta kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana.

Dakarun tabbatar da zaman lafiya a Darfur na majalisar dinkin duniya dana kungiyar tarayyar Afrika-AU wato Unamid sun kai kusan 20,000.