Kenya ta kulla yarjejeniya da China

  • 20 Agusta 2013
Kenyatta ya ce dangantakarsu da China gagarumin ci gaba ne ga Kenya

Jami'an kasar Kenya sun ce Shugaba Uhuru Kenyatta ya sanya hannu da takwaransa na kasar China, Xi Jinping, a kan wata yarjejeniya ta gina layin dogo da samar da makamashi da kare gandun daji wacce za a kashe dala biliyan biyar.

An sanya hannu kan wannan yarjeniya ce lokacin da Shugaba Kenyatta ya kai ziyararsa ta farko zuwa wata kasar waje tun bayan zabensa da aka yi a watan Maris.

Mista Xi ya ce karsashin da Kenyatta ke nunawa zai sanya kasar ta Kenya ta yi gagarumar bunkasa.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaba Kenyatta da kasashen yammacin duniya saboda yana fuskantar tuhuma kan zargin aikata laifukan cin zarafin bil-Adama a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague.

Nan gaba a cikin wannan shekarar ce za a yi masa shari'a a kotun bisa zargin haddasa rigingimun da suka barke bayan zaben shugaban kasar na shekarar 2007, koda yake ya sha musanta zargin.

Lokacin da Kenyatta ke yakin neman zabe a Kenya, kungiyar Tarayyar Turai ta ce ba za ta yi mu'amala da kasar sosai ba idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar.

Amurka ma ta gargadi kasar cewa za ta fuskanci mummunan sakamako idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Mista Kenyatta ya zarge su da yin katsadanlan a harkokin cikin gidan kasar, yana mai shan alwashin karfafa dangantaka da gabashin duniya.

Gina layin dogo

A wata sanarwa da ofishin Mista Kenyatta ya fitar, ya ce yarjejeniyar da kasar ta yi da China za ta kawo gagarumar bunkasa ga gwamnatinsa.

Sanarwar ta ambato Mista Kenyatta yana cewa, '' Layin dogon da za a shimfida yana da matukar amfani musamman ga yunkurin kasashen Gabashin Afirka na tabbatar da zurga-zurgar jama'a da kayayyaki cikin sauri''.

Layin dogon zai hada garin Malaba da ke kan iyaka da kuma Mombasa, mai tashar jiragen ruwa, daya daga cikin wuraren da aka fi gudanar da harkokin kasuwanci a Afirka.