BBC navigation

Jami'an Masar sun ce sun fitar da 'yan Uwa Musulmi daga masallacin Al-Fateh

An sabunta: 17 ga Agusta, 2013 - An wallafa a 16:33 GMT
Wani magoyin bayan Mursi

Wani magoyin bayan Mursi

Dakarun tsaro a Masar sun ce sun fitar da dukkan mutanen da suke cikin masallacin Al-Fathi dake birnin Alkahira, inda magoya bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi suka nemi mafaka.
Jan dagar a masallacin na Fathi ya dauki sa'o'i da dama, inda shaidu suka bayyana ganin amfani da bindigogi da barkonon tsohuwa.

Lokacin da soji ke ci gaba da yin kawanya ga masallacin, hotunan talabijin sun nuna jami'an tsaro suna zuwa ga hasumiyar masallacin.

Jiya da dare, soji sun shiga masallacin su nemi mutane su fita, wadanda suka fitan an rika dukansu - hakan ya sa saura suka ji tsoron ficewa.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.