Kotu ta tabbatar da hukunci kan Berlusconi

  • 1 Agusta 2013
Berlusconi
Akwai shari'u da dama a kan Silvio Berlusconi

Kotun kolin kasar Italiya ta amince da hukuncin daurin da aka yanke ma tsohon Fira ministan kasar, Silvio Berlusconi kan laifin zamba wajen biyan haraji.

Sai dai bisa la'akari da shekarunsa, da wuya ne Mr Berlusconi ya yi zaman jarun, maimakon haka mai yuwuwa a yi masa daurin talala ne a gidansa.

Ko kuma a sa shi ya yi wasu aikace aikace na yi wa al'umma hidima.

Hukuncin farko na kotun ya ce kamfaninsa na Mediaset ya kara farashin hakkin rarraba fina-finai, domin ya kaucewa biyan haraji.

Sai dai kotun ta umarci a sake duba hukuncin hana shi rike mukamin siyasa na shekaru hudu.

Masu sharhi na cewe Berlusconi yana karfin fada aji a fagen siyasar kasar, kuma akwai damuwar cewa dakatar da shi daga siyasa ka iya yin barazana ga gwamnatin hadakar kasar.